A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, wannan gini an gina shi ne da nufin nishadi da jin dadin mutanen Roma. Sai dai, wannan ba filin wasan motsa jiki ba ne; wuri ne kawai na kisan mutane da dabbobi don nishadin Romawa.
A cewar mutanen yamma da kansu, an kashe mutane sama da dubu dari biyar (500,000) da dabbobin daji sama da miliyan daya—kamar zakuna, kada, karkanda, har ma da giwaye—a cikin Colosseum domin nishadi kawai.
Idan muka kiyasta cewa wannan gini ya yi aiki na tsawon shekaru 200, lissafi zai nuna mana yawan mutanen da aka kashe a kowace rana. Shekaru 200 sun yi daidai da kwanaki 73,000. Idan aka raba mutane 500,000 da aka kashe da kwanaki 73,000, za mu sami mutum 6 zuwa 7 a kowace rana. Haka kuma, an kashe dabbobin daji 12 zuwa 13 a kowace rana har na tsawon shekaru 200.
Tunda yake tunani da falsafar yammacin duniya na yau sun samo asali ne daga tunanin falsafa, zamantakewa, tattalin arziki, da siyasar tsohuwar Girka da Roma, ba abin mamaki ba ne yadda kashe mutane don nishadi da kiyaye mulki ya zama ruwan dare a kasashen yamma, musamman Amurka.
Farfesa John Mearsheimer, fitaccen masanin kimiyyar siyasa a Jami'ar Chicago, ya yarda cewa Amurkawa sun kashe mutane sama da miliyan 38 a duniya tsakanin shekarar 1971 zuwa 2021, wato a cikin shekaru 50. Idan aka raba miliyan 38 da shekaru 50, za mu sami adadi mai ban tsoro: mutane 760,000 a kowace shekara.
Tambayar anan ita ce: Da wadannan alkaluma masu ban tsoro, ta yaya za mu amince da ikirarin kasashen yamma na kare hakin dan adam? Kamar yadda karin maganar Iran ke cewa: "Shin mu yarda da wutsiyar zakara (shaidar laifi) ko mu yarda da rantsuwar da kake yi?"
Tabbas, ba boyayye abu ba ne ga masu basira cewa a lokacin da Romawa—a matsayin alamar al'adun yamma—suke kashe mutane don nishadi, mutanen Iran masu wayewa da ilimi suna rubuta takardar hakin dan adam ta "Cyrus Mai Girma".
Wannan bayani ne na kadan daga cikin babban al'amari.
Ra'ayinka